Shugabanci ya inganta kadan a Afirka | Siyasa | DW | 03.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shugabanci ya inganta kadan a Afirka

A rahotonta na bana na shekara-shekara gidauniyar Mo Ibrahim ta ce an sami ci gaba kadan na mulki na gari a Afirka idan aka kwatanta da shekaru goma da suka wuce.

Jadawalin na Mo Ibrahim kan nazarin kasashen Afirka wajen aiwatar da shugabanci na gari shi ne irinsa mafi inganci a daukacin nahiyar. Rahoton ya yi nazarin kasashe 54 na tarayyar Afirka bisa matakai da suka hada da tsaro da kare hakkin bil Adama da zaman lafiya da kwanciyar hankali da gudanar da zabe na adalci da ingantaccen fannin shari’a. Sauran su ne fannin cin hanci da samar da muhimman ayyukan raya kasa da ci gaban al’umma da fannin kiwon lafiya da fatara da kuma Ilmi.

A jadawalin bana na nazarin shugabanci na gari, kasar Mauritius ce a kan gaba sai Botswana wadda ta zo ta biyu sai kuma Cape Verde da ta kasance ta uku. Sauran kasashen da ke biye su ne Namibia da Afirka ta kudu, yayin da kasashen da ake fama da rikici a cikinsu wadanda suka hada da Somaliya da Sudan ta kudu da kuma Jamhuriyar tsakiyar Afirka suka kasance kurar baya wajen aiwatar da shugabanci na gari.

Shugaban sashen kididdiga da nazarin cigaban kasashe a gidauniyar Mo Ibrahim wadda ta gudanar da binciken kuma babban sakatare a hukumar kula da tattalin arzikin Afirka Abdalla Hamdok ya yi bayani da cewa: "Idan ana maganar ci gaba, an sami dan kari a baki dayan jadawali shekaru da suka wuce zuwa yau daga kasha 49 zuwa 50. Ba wani ci gaban a zo a gani bane, amma abin da muka yi la’akari da shi, shine cewa al’amura basu tabarbare ba. Kuma mun bi diddigin wannan ne ta la’akari da tasiri da ya yi ga kasa ba wai sa hannu akan takarda ko zartar da manufa ta gwamnati ba. Haka kuma idan aka dubi ginshikai hudu na wanzuwar cigaba,an sami angizo a uku daga cikinsu". 

A waje guda dai kasashe 14 masu arzikin mai na Afirka basu tabuka wani abin a zo a gani ba a cewa jadawalin na Mo Ibrahim. Kasar Ghana ce kawai ta sami matsakaicin ci gaba idan aka kwatanta da sauran. Sai dai kuma duk da haka rahoton yace kasar ta Ghana ta fuskanci koma baya mafi muni ta fannin shugabanci tun shekarar 2006. Sauran kasashe kamar Najeriya da Algeria da Libya da Angola da kuma Gabon rahoton yace sun saki jiki basu yi wani tanadi ba na tunkarar yiwuwar faduwar farashin mai a kasuwannin duniya. 

Sauti da bidiyo akan labarin