1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Yemen ya yi murabus

Ahmed SalisuJanuary 22, 2015

Shugaban Yemen Abd-Rabb Mansur Hadi ya sanar da aniyarsa ta yin murabus daga mukaminsa 'yan sa'o'i kalilan bayan da firaministasa ya ajiye aiki.

https://p.dw.com/p/1EPHL
Abd Rabbo Mansur Hadi Präsident Jemen
Hoto: picture-alliance/C. Court

To sai dai jim kadan bayan da ya ajiye aiki, majalisar dokokin kasar ta ce ba ta amince da murabus din nasa ba. Gabannin bayyana ajiye aikin sa da Shugaba Hadin ya ce ya yi, firaministan kasar Khaled Bahah da majalisar ministocinsa sun mika masa takardunsu na ajiye aiki.

Firaministan da ministocin kasar dai sun ce sun ajiye aiki ne saboda abinda suka kira gudun shiga cikin takaddamar siyasa da yanzu haka kasar ke fama da ita. Gabannin daukar wannan mataki dai, 'yan kungiyar nan ta Houthi sun bukaci gwamnatin ta yi raba daidai da su na mukamai.

Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da 'yan bindiga na kungiyar ke cigaba da rike da wasu muhimman wurare a babban birnin kasar Sanaa ciki kuwa har da gidan shugaban kasar.