Shugaban Venezuela ya riga mu gidan gaskiya | Labarai | DW | 06.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Venezuela ya riga mu gidan gaskiya

Shugaban kasar Venezuela Hugo Chavez ya bar duniya yana da shekaru 58 da haihuwa, bayan shafe shekaru biyu yana jinyar chutar sankara.

Shugaban kasar Venezuela Hugo Chavez ya bar duniya yana da shekaru 58 da haihuwa, bayan shafe shekaru biyu yana jinyar chutar sankara. Marigayi Chavez ya kwashe shekaru 14 akan madafun ikon kasar da ke yankin Latin Amirka.

Mataimakin shugaban kasar Nicolas Maduro ya sanar da mutuwar shugaba Chavez. An bayyana kwanaki bakwai na zaman makoki, kuma za ayi jana'izar shugaban ranar Jumma'a mai zuwa. Tuni mutane su ka fito kan tituna domin nuna alhini ga Marigayi Shugaba Chavez. Sojoji sun bada tabbacin daukar matakan kare lafiya wajen fitowa kan tituna, tare da bada goyon bayan rundunar soja ga Nicolas Maduro wanda ya dauki madafun ikon kasar kafin gudanar da zabe cikin kwanaki 30 masu zuwa.

An haifi Marigayi Shugaban Venezuela Hugo Chavez cikin watan Yulin shekarar 1954, a Jihar Barinas na kasar kuma iyayensa malaman makaranta ne. Cikin shekarar 1975 ya kammala makarantar horas da hafsoshin soja. Ya yi koyarwa a makarantar a shekarar 1981.

A shekarar 1992, Chavez wanda ke mukamun Kanel a wannan lokaci, ya yi yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Carlos Andres Perez, ta hanyar juyin mulki, abun da ya janyo aka daure shi na tsawon shekaru biyu.

Tun bayan sake shi a shekarar 1994, Hugo Chavez ya kaddamar da jam'iyya, sannan ya lashe zaben shekarar 1998, aka rantsar da shi a shekarar 1999. Sojoji sun yi yunkurin kifar da gwamnatin Marigayi Chavez a shekara ta 2002, amma bayan kwanaki biyu boren da mutane su ka kaddamar ya sake dawo da shi kan madafun iko.

Yanzu mataimakinsa Nicolas Maduro ya zama shugaba na wucin gadi, kuma za a shirya zabe cikin kwanaki 30. Maduro shi ne dan takaran jam'iyya mai mulki, kamar yadda ministan harkokin wajen kasar ta Venezuela ya tabbatar.

'Yan adawa sun nemi shugaban majalisa Diosdado Cabello, ya karbi madafun ikon kamar yadda kundin tsarin mulki ya nuna.

Shugabanni da gwamnatocin kasashen duniya sun fara mika sakon ta'aziyyar rasuwar shugaban Venezuela Hugo Chavez, wanda ya bar duniya yana da shekaru 58.

Shugabar Brazil Dilma Rousseff ta ce wannan babban rashi ne ga daukacin kasashen Latin Amirka. Shugaban Ecudor Rafael Correa ya ce wannan rashi ne da za a dade ana tunawa. Kasashen Cuba da Argentina sun aiyana zaman makoki na kwanaki uku.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya ce Marigayi Shugaba Chavez ya yi aiki domin inganta rayuwar talakawan kasar da bada goyon bayan shirin samun zaman lafiya a Colombiya.

Kasar Amirka ta yi fatar mutuwar za ta kawo bunkasar demokaradiyya a kasar. Birtaniya ta mika nata sakon ta'aziyyar. Shugaban Faransa Francois Hollande ya ce Marigayi Chavez ya tabbatar da adalci kuma tarihi zai tuna da shi.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh