Shugaban Uganda ya yabi furicin Shugaba Trump kan Afirka | Labarai | DW | 23.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Uganda ya yabi furicin Shugaba Trump kan Afirka

Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya jinjina wa Shugaba Donald Trump na Amirka dangane da abin da ya kira gaskiya mai daci da Trump din ya fada kan kasashen Afirka wadanda ya bayyana da kasancewa kasashen wulakantattu.

A wani sakon da ya wallafa a wannan Talata a shafinsa na Tweeter Shugaba Museveni ya ce Shugaba Trump na birge shi saboda halinsa na fitowa fili ya tsage gaskiya komin dacinta ga kasashen Afirka da shugabanninsu a dai dai lokacin da shugabannin wasu kasashen ke yin kus-kus daga kas. 

Shugaba Museveni ya kara da cewa kalaman na Shugaba Trump kan nahiyar ta Afirka na kan turba, domin kasashen Afirkan ne ya kamata su iya shawo kan matsalolinsu da kansu, kuma laifi na 'yan Afirkan ne ba na wani ba, idan har suka kasa iya shawo kan raunin da kasashen nasu suke fuskanta shekaru da dama. 

Wadannan kalamai na Shugaba kasar ta Uganda wanda ke kan karagar mulkin kasarsa tun a shekara ta 1986 na zuwa ne a daidai lokacin da wasu shugabanni da ma al'ummomi na nahiyar Afirka ke ta tayar da jijiyoyin wuya na nuna rashin jin dadinsu da kalaman na Shugaba Trump, da suka bayyana a matsayin mai akidar wariyar launin fata.