Shugaban Tunisiya zai gana da ma′aikata | Labarai | DW | 13.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Tunisiya zai gana da ma'aikata

Shugaban kasar Tunisiya Beji Caid Essebsi ya bukaci tattaunawa da jam'iyun adawa da kungiyoyin fararen hula a wani mataki na kwantar da zanga-zangar adawa da tsarin gwamnati.

Wasu manyan birane Tunisiya sun barke da zanga-zanga mai tsanani na kusan kwanaki bakwai, da nufin nuna adawa da kara haraji da ya haifar da tsadar rayuwa sakamakon hauhawar farashin kayan abinci da sauran kayan masarufi.

Akalla mutum guda ya rasa ransa a zanga-zangar, amma 'yan sanda sun nesanta kansu da hannu a kisan. Sai dai a yanzu suna tsare da sama da mutane 800 ciki har da jagoran wata jam'iyar adawa bisa zargin tada zaune tsaye.

Tunisiya na shan fama da jerin zanga-zanga a kan karancin rashin ayyukan yi da talauci, abin da ake ganin zai dauki hankalin ganawar shugabannin kwadagon da shugaban kasar Beji Caid Essebsi.