Shugaban Tanzaniya na shakkun rigakafin COVID-19 | Labarai | DW | 28.01.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Tanzaniya na shakkun rigakafin COVID-19

Shugaban Tanzaniya John Magufuli ya fito a bainar jama’a yana kushe alluran rigakafin corona da Turawan yamma suka sarrafa. 

Duk da cewa kawo yanzu shugaban na Tanzaniya ya kasa kawo wata hujja da za ta gaskata ikirarin da yake yi, a ranar Laraba ya zargi mutanen kasar da suka yarda aka yi musu rigakafin corona a ketare da cewa sune suka kawo wa Tanzaniya zango na biyu na corona. 

Magufuli ya ce idan da rigakafin corona gaskiya ce da Turawa sun samar da rigakafin HIV/AIDS da Maleriya da kuma cutar daji, yana mai gargadin ‘yan Tanzaniya da kada su yarda Turawa su yi amfani da su wurin cimma wata manufa da sunan yaki da cutar corona. 

Tun daga tsakiyar shekarar da ta gabata dai lokacin da Tanzaniya ta sanar da cewa mutum 509 sun kamu da corona, gwamnatin kasar ba ta sake sabunta adadin masu kamuwa da cutar ba.