1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Sudan na ziyara a Masar

January 27, 2019

Shugaba Omar Hassan al-Bashir na kasar Sudan ya isa birnin Alkahira na Masar a wannan Lahadi, inda zai tattauna da takwaransa Shugaba Abdel Fattah al-Sisi, kamar dai yadda wasu majiyoyi a Masar suka tabbatar.

https://p.dw.com/p/3CHMg
Sudan Khartoum - Sudans Präsident - Omar Bashir
Hoto: picture-alliance/Xinhua News Agency/M. Khidir

Wannan ne ziyarar ketare karo na biyu da Shugaba al-Bashir ke yi, tun bayan da 'yan kasarsa suka fara zanga-zangar neman murabus dinsa tun cikin watan da ya gabata, lamarin kuma da ya kai ga asarar rayuka.

Al'umar Sudan dai na cewa ne sun gaji da mulkin Shugaba al-Bashir na kusan shekaru 30 a yanzu, da kuma suke fama da radadi a fannin tattalin arziki. 

Ana sa ran shugabannin biyu za su yi jawabi ga taron manema labarai, bayan ganawar da za su yi a yau.