Shugaban Rasha zai ziyarci kasar Masar | Labarai | DW | 09.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Rasha zai ziyarci kasar Masar

Shugaba Vladimir Putin na Rasha zai gana da takwaran aikinsa na Masar a birnin Alkahira don tattaunawa kan rikicin da kasashen Larabawa ke fuskanta.

Shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha zai kai ziyarar aiki a birnin Alkahira na Masar a daidai lokacin da kasarsa ke neman samun angizo a kasashen Larabawa.

Ziyarar ta kwanaki biyu za ta kasasnce ta farko da shugaban Rasha ya kai Masar a cikin shekaru goman da suka gabata. Sannan kuma na farko bayan da guguwar neman sauyi da ta yi awon gaba da kujerar mulkin Hosni Mubarak a shekar ta 2011.

Putin da Al Sisi mai masaukin baki, za su yi amfani da wannan dama wajen tattauna batutuwan da suka shafi rikicin Iraki da Syriya da ma rikicin da ke tsakanin Isra'ila da kuma Falesdinawa.