Shugaban Najeriya zai aiwatar da rahoton Amnesty | Labarai | DW | 12.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Najeriya zai aiwatar da rahoton Amnesty

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya yi alkawarin duba tare da tabbatar da abin da ya faru kan zargin take hakkin dan Adam da aka yi wa manyan habsoshin sojin kasar da ke yaki da Boko Haram

Shugaba Muhammadu Buhari na ya ba da tabbacin gwamnatinsa za ta duba rahoton kungiyar Amnesty International da ya zargi manyan mabsoshin soji da hannu bisa take hakkin dan Adam.

A cikin wata sanarwa da maitaimaka wa shugaban ta fadin yada labarai Garba Shehu ya fitar, Shugaba Buhari ya nuna damuwa da abin da ya faru, inda ya ce zai bincike gano gaskiyar abin da ya faru.

Shugaba Buhari ya ce binciken shi ne zai zama aiki na farko da yake gaban mutumin da za a nada a matsayin ministan shari'a. Sannan ya kara da cewa gwamnatinsa za ta yi biyayya bisa batutuwa na kare hakkin dan Adam.