Shugaban Najeriya yayi kira da a sako maaikatan mai da aka sace | Labarai | DW | 18.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Najeriya yayi kira da a sako maaikatan mai da aka sace

Yan takifen yankin Naija Delta da suka sace maaikatan mannan yan kasar waje sunyi barazanar kaddamar da wasu jerin munanan hare hare a yan kwanakinnan masu zuwa.

A wata sanarwa da suka fidda kungiyar yantakifen mai suna kungiyar yanto yankin Naija Delta tace daga ranar daya ga watan Fabrairu mai zuwa zata kara azamar hare haren akan maaikatan mai da iyalansu muddin dai basu kwashe inasu inasu sun bar yankin ba kafin wannan lokaci.

A baya bayan nan an ruwaito shugaban Najeriyar Olusegun Obasanjo yana rokon wadanda suka sace maaikatan da su sako su.