Shugaban Mauritaniya ya koma gida | Labarai | DW | 25.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Mauritaniya ya koma gida

Dubban mutane sun fito titunan Nouakchott babban birnin ƙasar Mauritaniya, domin tarbar Shugaba Ould Abdel Aziz

Dubban mutane sun fito titunan Nouakchott babban birnin ƙasar Mauritaniya, domin tarbar Shugaba Mohamed Ould Abdel Aziz, wanda ya yi jinya a asibitin ƙasar Faransa, bayan harbinsa bisa kuskure da wani jami'in tsaro ya yi.

Mutanen sun yi dafifi tun daga filin saukar jiragen sama zuwa cikin birnin, saboda maraba wa shugaban, wanda ya kwashe makonni shida yana jinya.

Shugaban ya koma gida ranar Asabar, 24.11.2012- abun da ya kawo ƙarshen jita-jitar game da lafiyar shugaba Abdel Aziz ɗan shekaru 55 da haihuwa.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita:Halima Balaraba Abbas