1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba IBK na Mali ya yi nassara a zaben kasar

Salissou Boukari
August 16, 2018

Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita, mai shekaru 73 da haihuwa, ya yi nassara a zaben shugaban kasar da ya gudana zagaye na biyu inda ya samu kashi 67,17 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada.

https://p.dw.com/p/33Gk0
Mali neuer Präsident gewählt Ibrahim Boubacar Keita
Shugaba Ibrahim Boubacar Keita na MaliHoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Shugaban mai ci na kasar ta Mali ya yi nasar ce a gaban abokin takararsa Soumeila Cisse na bangaran adawa, wanda ya samu kashi 32, 83 cikin 100. Hakan zai bawa shugaban da 'yan kasar ke kiran shi da sunan IBK damar yin wani sabon wa'adin mulki na biyu.

Da dama dai na kallon shugaba Boubakar Keita, wanda aka haifa a garin Koutiala da ke kudancin kasar ta Mali kusa da Burkina Faso, a matsayin mai kyauta, amma da saurin fushi da kuma nuna bangaranci, wanda a wa'adin mulkinsa na farko na shekara biyar, ya sauya firaminista har sau biyar, sannan daga cikin abokan takararsa 23 a zagayan farko na zaben, akwai da dama da suke tsaffin ministocinsa ne abin da ke nuni da yadda shugaban ke da wuyar sha'ani.

A wa'adin farko an zabi shugaban kasar ta Mali ne da kashi 77,6 cikin 100, amma kuma a cewar masu adawa da mulkinsa hakan bai sa shi yin wani abin azo a gani kan mahimman batutuwan da suka addabi 'yan kasar ta Mali ba.