1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawar shugabannin Amurka da Koriya ta Kudu

Zulaiha Abubakar
May 23, 2018

Shugaban kasar Amirka Donald Trump ya karbi bakuncin takwaransa na kasar Koriya ta Kudu Moon Jae-In don cigaban tattaunawa a kan lalata makaman kare dangin kasar Koriya ta Arewa .

https://p.dw.com/p/2y9Vz
Trump und Moon Jae In Washington
Hoto: Getty Images/AFP/S. Loeb

Wannan ganawa dai na zuwa ne a daidai lokacin da alamu ke nuni da cewar babu tabbacin yiwuwar babban taron da za a gudanar a watan Yuni tsakanin shuwagabannin kasashen na Amirka da Koriya ta Arewa.

Da yake tsokaci a kan batun babban taron Shugaba Trump ya bayyana cewar yana da tabbacin Kim Jong Un ya dauki aniyar lalata makaman kare dangin da kasar ta Koriya ta Arewa ta mallaka.

A nasa bangaren Shugaba Moon na Koriya ta Kudu ya yabawa shugaban kasar ta Amirka bisa irin canjin da Koriya ta Arewa ta samu cikin kankanin lokaci.