Shugaban Koriya ta Kudu ya gana da na Arewa | Labarai | DW | 26.05.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Koriya ta Kudu ya gana da na Arewa

Shugaban kasar Koriya ta Kudu Moon Jae-in ya gana da takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong Un a yankin nan da babu sojoji da ke tsakanin kasashen biyu a cewar fadar shugaban na Koriya ta Kudu.

Wannan ganawa na zuwa ne kwana daya bayan sanarwar shugaban Amirka Donald Trump na cewa akwai alamun haduwarsu da shugaban na koriya ta Arewa za ta wakana. Shugabannin biyu sun tattauna na tsawon awoyi biyu a Panmunjon, inda suka yi wancan haduwa ta farko a watan da ya gabata, har ma suka yi sanarwa ta hadin gwiwa da ke cewa za su inganta hulda a tsakanin kasashen biyu.

Sanarwar fadar shugaban na Koriya ta Kudu ta kara da cewa, shugabannin biyu sun tattauna hanyoyin bi don aiwatar da abubuwan da suka tsaida tare, sannan da kuma ganin babbar haduwar da za a yi tsakanin Koriyoyin biyu da shugaban Amirka ta wakana kamar yadda aka tsara ta.