1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Koriya ta Arewa na ganawa da shugaban China

Suleiman Babayo
May 8, 2018

Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa ya sake ganawa da Shugaba Xi Jinping na China gabanin tattaunawa da shugaban Amirka.

https://p.dw.com/p/2xMEe
China Ministerpräsident Xi Jinping emfängt norkoreanischer Präsident Kim Jong Un
Hoto: picture-alliance/dpa/XinHua/Ju Peng

Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa ya kai ziyara China inda ya gana da Shugaba Xi Jinping a karo na biyu. Kafofin yada labaran China sun ce an yi wannan ganawa ta ba zata a garin Dalian na yankin arewa maso gabashin kasar ta China.

Lamarin da yake zuwa gabanin ganawa da aka tsara tsakanin Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa da kuma Shugaba Donald Trump na Amirka cikin makonni masu zuwa, game da neman hanyoyin dakile shirin kasar Koriya ta Arewa kan bunkasa makamun nukiliyar kasar.