Shugaban Kenya Kibaki na kan gaba a zaɓen shugaban ƙasar | Labarai | DW | 28.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Kenya Kibaki na kan gaba a zaɓen shugaban ƙasar

Sakamakon farko na zaben shugaban ƙasa da na ´yan majalisar dokoki da aka gudanar jiya a ƙasar Kenya na nuni da cewa shugaba Mwai Kibaki na kan gaba da kashi 47.3 ciki 100 idan aka kwatanta da kashi 42.8 cikin 100 da shugaban ´yan adawa Raila Odinga ya samu. A wani lokacin yau juma´a ake sa ran cewa hukuma zata ba da sakamakon wannan zaɓe. Dukkan ´yan takarar biyu sun yi alƙawarin daukar matakan farfaɗo da tattalin arziki tare da ba da ilimi kyauta daga matakin firamare har zuwa sakandare. Rahotanni sun ce mutane sun fita ƙwansu da kwarkwarta don kaka ƙuri´a sannan an samu dogayen layuka a tashoshin zaɓe. Masu sa ido a zaɓe fiye da dubu 15 na ƙungiyar tarayyar Turai da wasu yankuna na duniya suka ga yadda zaɓukan suka gudana.