shugaban kasar Iraqi yace ya fara tattaunawa da kungiyoyin yan tawaye na Iraqi | Labarai | DW | 30.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

shugaban kasar Iraqi yace ya fara tattaunawa da kungiyoyin yan tawaye na Iraqi

Shugaban kasar Iraqi Jalal Talabani yace ya kusa cimma yarjejeniya da wasu kungiyoyin sojin sa kai guda 7,wanda hakan zai iya kawo karshen tashe tashen hankula a kasar.

Yace Amurka ta fara tattaunawa da wadannan kungiyoyi tare da amincewarsa,kuma akwai yiwuwar cimma yarjejeniya.

Yace kungiyoyin suna adawa da mamayar da Amurka tayiwa Iraqi,saboda haka zaa tattauna dasu kuma zasu iya shiga harkokin siyasa na kasar.

Shugaban na Iraqi ya kuma zargi kasar Syria makwabciya,da laifin barin sojin haya shiga kasar ta Iraqi.