1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban kasar Iran ya kara baro ta ,a game da game da nuna kyamar Isra´ila

December 14, 2005
https://p.dw.com/p/BvGW

Shugaban kasar Iran Mahamud Ahmadinijdad, ya kara cyaba kalamomin da ya yi ,a kwanaki baya, na haramta kasar Israela.

A wani saban jawabi mai tsauri, da ya gabatar yau, ya ce sam, bai amince ba ,da batun cewar wai an yi wa yahudawa kissan kiyasu a lokacin yaki dunia na 2.

Ya suka da kakkausar halshe, ga kasashen da ke daurewa Israela gindi, ta na ci karen ta, ba babbaka.

Ya kuma yi tsaye kann bakan sa na cewar kamata tayi ,kasasheh turai, da Amurika, ko kuma Kanada, su tsunguya wa Yahudawa hili, a yankunan su, domin su girga haramtatar kasar Isra´ila, kamar yadda ya fada.

A wani bangare na jawabin nasa, Mahamud Ahmadi Nedjad, ya ce ko da mafarki ,Iran ba za ta ja da baya ba, daga manufofin ta,na kira makaman nuklea, domin kariyar kanta daga barazanar kasashe azzalumai.

A yayin da al´umar kasar Iran ta nuna goyan baya ga wannan jawabi, kungiyar gamayya turai Allah wadai ta yi da shi, haka zalika kasar Amurika.

Jawabin ya zo a yayin da ya rage kwanaki kalilan, a koma tebrin shawara ,tsakanin Iran ga Kungiyar EU, a game da makaman nuklea.