1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Xi Jingping na China a Afirka

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 21, 2018

Shugaban kasar China Xi Jinping ya fara wata ziyara a kasashen Afirka da nufin bunkasa dangantakar soji a tsakanin Chinan da Afirka.

https://p.dw.com/p/31rxT
China Xi Jingping
Shugaban kasar China Xi JingpingHoto: Getty Images/W.Zhao

Xi dai zai ziyarci kasashe hudu a wannan ziyara tasa, inda zai fara isa Senegal daga nan sai kasar Ruwanda kafin daga bisani a ranar Laraba ya isa Afirka ta Kudu domin halartar taron kungiyar kasashe da tattalin arzikinsu ke bunkasa cikin hanzari ta BRICS, da suka hadar da Brazil da Rasha da Indiya da China da kuma Afirka ta Kudu. Xi dai zai kammala ziyarar tasa ne a Tsibirin Mauritius. Ziyarar Xi dai na zuwa ne a daidai lokacin da Chinan ke fuskantar gagarumar hamayya a fannin kasuwanci daga gwamnatin Shugaba Donald Trump na Amirka, wanda gwamnatinsa ba ta damu sosai da kulla alaka da nahiyar ta Afirka ba, yankin da ke zaman na biyu mafi yawan al'umma a duniya.