Shugaban kasar Benin ya rusa gwamnati
August 9, 2013Shugaban Jamhuriyar Benin Dr Thomas Yayi Boni ya rusa gwamantinsa.
Kamfanin dullancin labarun Reuters da ya ruwaito wannan labari, ya ce sanarwar da fadar shugaban ta baiyana, ta ce Dr Yayi Boni, ya dauki wannan mataki, domin sabinta Majalisar Ministoci, wadda ya girka shekaru biyu kenan da suka gabata, lokacin da aka zabe shi a wa'adin mulki na biyu.
Russasar gwamnatin, ta kunshi ministoci 26, wanda ake zargin cewa sun fara hukewa, wajen gudanar da aiyukan kasa.
A cikin mako mai zuwa, ake sa ran shugaban kasar Benin, zai kafa sabuwar gwamnati.
Jamhuriyar Benin na daya daga kasashen Afirka kalilan, da suka fara cin gajiyar mulkin demokradiyar da aka kafa a shekara 1990.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Usman Shehu Usman