Shugaban kasar Amirka ya bayyana shakku game da Isra′ila | Labarai | DW | 11.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban kasar Amirka ya bayyana shakku game da Isra'ila

Donald Trump ya bayyana shakkunsa akan sahihancin niyar kasar Isra'ila ta sulhuntawa da Falasdinu.

Donald Trump ya kuma kara da cewar duk da cewar akwai kyakyawar dangantaka tsakanin Amirka da Isra'ila,sulhuntawa da Falasdinawa za ta kara dankon alakar kasashen biyu. A baya dai shugaba Trump ya yi Allah wadai da Falasdinawa lokacin da su ka shaidawa duniya cewar ba bu sauran batun sulhu tsakanin su da Isra'ila bayan bayana birnin  Kudus a matsayin babban birnin kasar ta Isra'ila.