1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabancin CDU zai yi murabus

Abdul-raheem Hassan
October 7, 2021

Armin Laschet shugaban jam'iyar CDU ta Angela Merkel, ya nuna alamar yin murabus daga shugabancin jam'iyyar masu ra'ayin mazan jiya, bayan gaza samun nasara a zaben 'yan majalisun dokoki da ya bar su a gefen 'yan adawa.

https://p.dw.com/p/41PvK
Nach der Bundestagswahl I Armin Laschet I CDU
Hoto: Ina Fassbender/AFP

Armin Laschet ya gayawa manema labaru cewa za su gaggauta magance matsalar CDU ta hanyar jagorancin jam'iyyar zuwa kwamitin zartarwa na tarayya, ya kara da cewa zai gabatar da ranar da za a gudanar da babban taron jam'iyyar don warware wadannan batutuwa.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da aka dage cigaba da tattaunawar kulla kawance zuwa makon gobe inda ake fatan cimma dai-daiton kafa gwamnati.