Shugaban Italiya ya rusa Majalisar Dokoki | Labarai | DW | 22.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Italiya ya rusa Majalisar Dokoki

Bayan murabus ɗin Mario Monti,za a shirya zaɓen 'yan majalisa a Italiya cikin watan Faburairu na shekara 2013.

epa03498535 The President of the Italian Senate Renato Schifani (top 2-R) announces the result of the confidence vote in the Senate on a government economic-development bill, in Rome, Italy, 06 December 2012. The centre-left Democratic Party (PD) said the same day that Premier Mario Monti must consult with Italian President Giorgio Napolitano as his emergency technocrat government has effectively lost its majority in parliament. The call came after former Italian Prime Minister Silvio Berlusconi's People of Freedom (PdL) party announced it was deserting the confidence vote in the Senate on a government economic-development bill. 'If the government no longer has a majority, I think Monti should go to (see Napolitano at) the Quirinal Palace,' said Anna Finocchiaro, the PD's Senate whip. The government won the confidence vote as it was backed by the other parties supporting Monti's government, including the PD and the centrist UDC, and the PdL, the biggest group in parliament, did not actively vote against it. EPA/GIUSEPPE LAMI

Majalisar Dokokin Italiya

Shugaban ƙasar Italiya Giorgio Napolitano ya rusa Majalisar Dokokin ƙasar, bayan murabus ɗin Firaminista Mario Monti a ranar Juma'a. Monti ya yi watanni13 ya na shugabancin gwamnatin Italiya, kuma masana harkokin tattalin arziki, sun ce ya yi nasarar kuɓuto ƙasar daga bala'in talauci. Ya zuwa yanzu, ba a san ko tsofan Firaministan ba, zai shiga takara a zaɓen 'yan majalisa, wanda za a shirya a watan Faburairu na shekara mai kamawa.

A ranar Lahadi Profesa Mario Monti zai baiyana matsayinsa, game da shiga takara a wannan zaɓe. A halin yanzu dai, ya samu goyan baya daga jama'a da dama, dake ɗaukarsa a matsayin wanda zai iya fidda surfe daga ruwa.

Sai dai idan kuma ya yanke shawarar ƙin shiga takara, 'yan siyasar ƙasar Italiya sun nuna buƙatar Mario Monti ya cigaba da mulkin riƙwan ƙwarya har bayan zaɓe.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita:Mohammad Nasiru Awal