Shugaban Iraki ya koma gida | Labarai | DW | 19.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Iraki ya koma gida

Bayan shafe tsawon lokaci yana jinya Shugaba Jalal Talabani na Iraki ya isa gida

Shugaban kasar Iraki Jalal Talabani ya isa gida a yau Asabar bayan da ya shafe shekara guda da rabi yana karbar magunguna a wani asibiti a Jamus, sakamakon bugun zuciya. Shugaban ya isa kasar ne a daidai lokacin da rikici ke cigaba da ta'azara. Mai shekaru 80 na haihuwa kuma daya daga cikin yan siyasar Kurdawa ya sauka ne a filin jirgin saman Kurdistan, kuma hukumomin yankin sun ce Talabani ya umurci cewa kada a yi wani buki dan dawowarsa bisa la'akari da rikicin da ke faruwa.

Ranar Talatar da ta gabata majalisar dokokin kasar ta zabi kakakinta, a wani matakin da ake gani zai taimaka wajen dakile dambarwar siyasar da ya mamaye zaben wadanda za su kasance a mahimman mukamamn kasar guda uku.

Dokokin da aka gindaya bayan mamayar da Amirka ta yi wa kasar ta Iraki a shekara ta 2003 sun tanadi yin la'akari da mahimman bangarorin kasar guda uku wajen zaben wadannan mutane, inda wajibi ne kakakin majalisa ya kasance dan Sunni, firaminista dan Shi'a sai kuma shugaban kasa Bakurde.

Majalisar za ta zauna ranar Laraba, amma ba a tantance ranar da za ta yi zaben firaminista ba.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Suleiman Babayo