shugaban hukumar jin kai na majalisar dinkin duniya ya isa Sudan | Labarai | DW | 07.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

shugaban hukumar jin kai na majalisar dinkin duniya ya isa Sudan

Shugaban hukumar jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya,Jan Egeland ya isa kasar Sudan,inda yayi kira da a baiwa maaikatan agaji karin damar shiga yankin Darfur,kamar yadda aka amince bisa yarjejeniyar kawo karshen yakin shekaru 3 a yankin.

Ana sa ran Egeland zai tattauna da gwamnatin Sudan wadda tayi alkawarin sake gina yankin na Darfur.

Karkashin yarjejeniyar ne kuma,zaa dauki yan tawaye 5,000 cikin rundunar tsaro ta Sudan.