1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shugaban Guinea-Bissau ya sanar da ranar yin zaben majalisa

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
July 9, 2024

Shugaba Embalo da ke kan karagar mulki tun a shekarar 2020, ya rushe majalisar dokokin wadda 'yan adawa suka fi rinjaye a cikin watan Disamban bara, bisa zarginsu da yunkurin yi masa juyin mulki

https://p.dw.com/p/4i2aS
Hoto: Yelena Afonina/TASS/picture alliance

Shugaba Guinea-Bissau, ya sanar da shirin gudanar da zaben majalisar dokokin kasar, a ranar 24 ga watan Nuwamba mai zuwa, watanni kalilan bayan rushe ta da ya yi, sakamakon zargin yunkurin hamabarar da shi daga kan karagar mulki.

karin bayani:Umaro Sissoco Embalo

Wannan dai shi ne karo na biyu cikin shekara daya da rabi da za a gudanar da zaben majalisar dokokin, a wannan kasa mai tarihin fama da juyin mulki, tun bayan samun 'yancin cin gashin kai daga kasar Portugal a shekarar 1974.

Karin bayani:An yi yunkurin juyin mulki a Guinea Bissau

Shugaba Embalo da ke kan karagar mulki tun a shekarar 2020, ya rushe majalisar dokokin wadda 'yan adawa suka fi rinjaye a cikin watan Disamban bara, bisa zarginsu da yunkurin yi masa juyin mulki, lamarin da ya janyo tarzoma a kasar, tare da asarar rayuka.