Shugaban Ghana zai yi rantsuwar fara aiki | Labarai | DW | 07.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Ghana zai yi rantsuwar fara aiki

A wannan Litinin ake rantsar da Shugaban Ghana John Dramani Mahama, domin fara sabon wa'adin mulki duk da kalubalantar sakamakon zaben da bangaren adawa ke yi.

A wannan Litinin ake rantsar da Shugaban Ghana John Dramani Mahama, domin fara sabon wa'adin mulki, sakamakon lashe zaben watan jiya na Disamba da ya yi.Cikin watan Juli Mahama ya zama shugaba na riko, bayan mutuwar Marigayi Shugaba Farfesa John Attah Mills ta kwatsam. Kuma tuni shugaban ya yi kirar neman hadin kai, sakamakon yadda babban dan takaran jam'iyyar adawa Nana Akufo-Addo, ke kalubalantar sakamakon zaben.

A birnin Accra fadar gwamnatin kasar, cikin wani biki ake sa ran Shugaba Dramani Mahama zai yi rantsuwar ta fara sabon wa'adin mulki na shekaru hudu.Kasar ta Ghana da ke yankin yammacin Afirka, ana yaba mata saboda kwanciyar hankali ta fuskan siyasa da ake samu.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe