Shugaban Faransa ya nemi ganin an taimaka wa Ƙurdawa | Labarai | DW | 14.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Faransa ya nemi ganin an taimaka wa Ƙurdawa

Shugaba Francois Hollande na Faransa ya buƙaci haɗa ƙarfi wajen yaƙi da 'yan ta'addan IS

A wannan Talata Shugaban Faransa Francois Hollande ya nemi ƙasashen da abin da ya shafa da su taimaka da makamai wa ƙawancen yaƙi da 'yan Ƙungiyar IS masu da'awar neman kafa daular Musulunci. Sannan ya buƙaci ƙasar Turkiya ta buɗe kan iyaka domin taimakon 'yan Kobani da suka galabaita.

Wannan kalaman sun zo lokacin da rahotanni ke nuna cewar dakarun Ƙurdawa sun samu nasarar fatattakar 'yan Ƙungiyar ta IS daga wani tsauni mai mahimmanci na yankin, kuma sun samu nasarra da taimakon jiragen saman yaƙi na kawance da Amirka ke jagoranta, wadanda suka yi barin wuta wa tsagerun.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita : Abdourahamane Hassane