Shugaban Faransa ya cika kwanaki 100 | Siyasa | DW | 21.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shugaban Faransa ya cika kwanaki 100

Emmanuel Macron ya cika kwanaki 100 a karagar mulki, sai dai kuma tuni farin jininsa ya fara dusashewa sabanin yadda jama'a suka rika begensa da farko.

Alkaluman kididdiga na cibiyar binciken ra'ayin jama'a, IFOP sun nuna farin jinin shugaban na Faransa ya tsaya ne a 36 cikin dari wanda ke zama adadi mafi karanci idan aka kwatanta da shugabanni da suka gabace shi kamar Sarkozy da Francois Hollande.

Raguwar farin jinin Macron ya kara baiyana ne a 'yan makonnin da suka gabata yayin da masu sukar lamiri ke cewa karfin mulki ya fara hawa kan shugaban inda ya fara daukar salo irin na kama karya.

Takaddamar da ta wanzu a bainar jama'a tsakanin matashin shugaban mai shekaru 39 Emmanuel Macron da babban hafsan sojin kasar ta Faransa Janar Pierre de Villiers kan matakan tsimi na rage kasafin kudin rundunar soji, ta rage kimar shugaban a idanun Faransawa. A sakamakon wannan jayayya ne kuma babban hafsan sojin ya ce ya ajiye aiki.

Ko da yake Emmanuel Macron ya yi aiki a matsayin kwararre kuma ministan tattalin arziki a karkashin Francois Hollande, ya sha baiyana ra'ayin da ya sha bambam da na 'yan siyasar Faransa. To ko yaya masana ke kallon kamun ludayinsa kawo yanzu? Farfesa Frank Baasner na cibiyar nazari ta Jamus da Faransa da ke Berlin ya yi tsokaci ya na mai cewa:

Frankreich Parlamentswahlen Emmanuel Macron (Getty Images/AFP/P. Huguen)

Macron dai na da tarin kalubale a gabansa

" Kwanaki 100 ana iya cewa suna da tsawo a lokaci guda kuma ana iya cewa basu da tsawo. Mutum ba zai yi tsammanin shugaban da yake da zaben 'yan majalisa a gabansa da nauyi na kafa gwamnati ya iya gudanar da wani abu cikin watanni uku ba. Amma kuma ana iya jinjina masa cewa dukkan abin da ya yi alkawari ya cika su. A saboda haka ina jin ya na kan turba."

A yanzu haka dai ana kan tattaunawa da kungiyoyin kwadgo akan matakan garanbawul ga fannin kwadon, wanda yake so ya aiwatar a watan Satumba, yayin da a badi kuma yake son aiwatar da kwaskwarima ga dokar fansho, da zai tsame wani rukuni na jama'a da ake gani masu hali ne daga karbar fansho a gwamnati, lamarin da ake gani batu ne mai sarkakiya kamar yadda Farfesa Baasner ya nunar:

" Wannan a ra'ayina ina ganin zuwa badi zai yi wuya, amma idan aka sami raguwar marasa aiki, tattalin arziki ya habaka, to a nan Macron na iya bugun kirji ya ce na yi kwaskwarimar da ta dace wadanda ya kamata a cigaba da su, nasarar mu ce baki daya."

Wani abu kuma da ya yiwa shugaban tabo shi ne rage Euro biyar cikin alawus na gida da ake bayarwa, tambayar ita ce idan za'a yi korafi kan ragin Euro  biyar to yaya kuma ga ragi mai yawa?.

Matashin shugaban dai ya karbi ragamar mulki a lokaci mawuyaci. Tun daga watan Nuwamba na shekarar 2015 kasar ke cikin dokar ta baci sakamakon harin ta'addanci da aka kai gidan rawa na Bataclan, sai dai a ranar daya ga watan Nuwamba Macron ya dage dokar ta bacin.

Frankreich Emmanuel Macron & Petro Poroschenko (Reuters/P. Wojazer)

Emmanuel Macron da Petro Poroschenko na Ukraine

A lokacin yakin neman zabe dai Macron ya gabatar da manufarsa kan ministan kudi na tarayya Turai da kuma shawararsa kan kasafin kudin kasashen masu amfani da kudin Euro. Har kafin gudanar da zaben majalisun dokokin Jamus dai babu abin da zai sauya dangane da wannan ra'ayi.

Jama'a dai sun yi na'am da imanin da shugaban ke da shi akan shugabancin Tarayyar Turai a Brussels da kuma kyakkyawar dangantakarsa da shugabanni da gwamnatoci na kasashen waje.

 

Sauti da bidiyo akan labarin