1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Kafofin watsa Labaru

Shugaban Tashar-DW ya samu karin wa'adi

Suleiman Babayo
September 28, 2018

Peter Limbourg ya samu karin wa'adin mulki na shekaru shida a karo na biyu lokacin da majalisar gudanarwa ta kafafen yada labaran Jamus ta yi zabe.

https://p.dw.com/p/35ekL
DW Mitarbeiterporträt Intendant Peter Limbourg
Hoto: DW/M. Müller

Peter Limbourg ya samu nasarar ci gaba da jagorancin Tashar-DW. A zaben da majalisar gudanarwa ta kafafen yada labarai ta gudanar a birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus, an amince da tsawaita mukumin ga mai shekaru 58 da haihuwa lokacin da aka kada kuri'a. Shi dai Limbourg ya kasance dan takara daya tilo.

An kada kuri'ar shekara guda gabanin karewar wa'adinsa na farko na shekaru shida, wanda zai kawo karshe 30 ga watan Satumba na shekara mai zuwa ta 2019. Karkashin shugabancin Limbourg Tashar-DW ta samu gagarumin fadada a tashar talabijin da rediyo gami da intanet.