1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ko Alassane Ouattara za yi takara a zaben 2020?

Abdourahamane Hassane
June 2, 2018

Shugaba Alassane Ouattara na Cote d'Ivoire wanda wa'adin mulkinsa ke kanmala a shekara ta 2020 ya ce bai fitar da sa ran cewar ba zai tsaya takara a karo na uku.

https://p.dw.com/p/2yqul
DW Elfenbeinküste Versöhnung
Hoto: DW/K. Gänsler

Hakan kuwa na faruwa ne a dai dai lokacin da ake fadi tashin ganin wanda zai gaje shi a matsayin na shugaban kasa an tabbatar da shi. A cikin wata hira da jaridar Jeune Afrique ta yi da shugaban na Cote d'Ivoire ya ce sabon kudin tsarin mulkin kasar ya ba shi damar yin takara daga shekara ta 2020. Sai dai kuma magoya bayan jam'iyyar PDCI na ganin cewar a shekara ta 2020 yakamata a ce shugaban kasa ya fito daga banganransu.