Shugaban China Telecom ya yi murabus | Labarai | DW | 30.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban China Telecom ya yi murabus

Kwanaki uku kenan da hukumomin China suka kaddamar da bincike kan Chang Xiaobing, dangane da zargin cin hanci da karbar rashawa da ake masa.

Hukumar kula da yaki da cin hanci ta kasar wadda ta sanar da wannan labarin, ta ce a yanzu haka ana gudanar da bincike akan Chang Xiaobing kan wasu laifuffuka masu tsanani da ke da nasaba da cin hanci da karbar rashawa.

A yanzu haka dai Mr. Chang na kuma fuskantar binciken cin hanci a China Unicom inda ya rike mukamin shugaba tun da farko, kafin daga bisani ya zama babban darekta na China Telecom.

Tun bayan hawansa karagar mulki ne dai shugaban China Xi Jinping, ya kaddamar da gagarumin aiki na yaki da cin hanci da karbar rashawa, batu da ya ritsa da manyana jami'an gwamnatin kasar masu yawa da shugabannin kamfanoni masu zaman kansu.