Shugaban China Hu Jintao ya fara wani rangadi a nahiyar Turai | Labarai | DW | 08.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban China Hu Jintao ya fara wani rangadi a nahiyar Turai

Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya isa Birtaniya a matakin farko na rangadin da ya ke kawo wasu kasashen Turai. Hade da wani gagarumin faretin soji, Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu ta tarbe shugaban na China lokacin da yake fara ziyarar aiki ta yini 3 a Birtaniya. Daruruwan mutane sun gudanar da zanga-zangar sukar lamirin China dangane da mamaye yankin Tibet da kuma keta hakkin bil Adama a cikin kasar. A ranar alhamis mai zuwa ake sa ran isowar Hu Jintao a nan Jamus, sannan ya gana da shugaban gwamnati mai barin gado Gerhard Schröder a ranar juma´a, kafin su dasa harsashen ginin wata cibiyar yada al´adun China ta farko a cikin kasar ta Jamus. Shugaban na China zai kuma kai ziyarar aiki a Spain.