Shugaban Amirka yana fara ziyara a kasashe biyu na nahiyar Afirka | Labarai | DW | 24.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Amirka yana fara ziyara a kasashe biyu na nahiyar Afirka

Ana sa ran dubban mutane za su tarbi shugaban Amirka lokacin da ya fara ziyara a kasashen Kenya da Habasha.

Shugaba Barack Obama na kasar Amirka a wannan Jumma'a zai fara ziyarar aiki zuwa kasar Kenya da ke yankin gabashin Afirka, inda ke zama mahaifar mahaifinsa.

Shugaban zai halarci taron kasuwanci sannan ya gana da Shugaba Uhuru Kenyatta na kasar ta Kenya. Dubban mutane ake sa ran za su tarbi shugaban wanda suke dauka a matsayin dan-uwa.

Ranar Lahadi Shugaba Barack Obama na Amirka zai wuce zuwa kasar Habasha inda zai yi jawabi a helkwatar kungiyar kasashen Tarayyar Afirka da ke birnin Addis Ababa.