Shugaban Amirka ya isa Habasha a mataki na biyu na ziyara a kasashen Afirka | Labarai | DW | 27.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Amirka ya isa Habasha a mataki na biyu na ziyara a kasashen Afirka

Shugaba Obama na Amirka zai gana da manyan jami'an gwamnatin Habasha tare da jawabi a helkwatar kungiyar Tarayyar Afirka

Shugaba barack Obama na kasar Amirka yana isa kasar Habasha a mataki na biyu na ziyara a kasashen Afirka, inda ya fara da kasar Kenya da ke zama mahaifar mahaifinsa.

Shugaba ya samu kekkyawar tarba lokacin da ya isa birnin Addis Ababa fadar gwamnatin kasar Habasha, inda birnin ya sha ado da hotunan Obama tare da sakonni yi masa maraba.

Shugaba Obama zai tattauna da Firaministan Habasha da sauran manyan jami'an gwamnati tare da jawabi a helkwatar kungiyar Tarayyar Afirka.