Shugaban Amirka ya gabatar da jawabi a gaban kungiyar Tarayyar Afirka | Labarai | DW | 28.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Amirka ya gabatar da jawabi a gaban kungiyar Tarayyar Afirka

Shugaba Obama na Amirka ya nemi tashi tsaye domin kawo karshen matsalolin cin hanci da rikice-rikice wadanda suka hana nahiyar Afirka bunkasa

Shugaba barack Obama na kasar Amirka ya gabatar da jawabi a helkwatar kungiyar Tarayyar Afirka da ke birnin Addis Ababa na kasar Habasha cikin ziyarar mataki na biyu na kasashen nahiyar. A cikin jawabi Obama ya nemi kasashen Afirka su tashi tsaye wajen kawar da cin hanci da rashawa da suka yi wa nahiyar katutu tare da dakile duk wani ci-gaba da ake bukata. Sannan ya nemi ganin ci gaba da yaki da ta'addanci da shawo kan rikice-rikice da ake samu a wasu kasashen nahiyar.

Shugaba Obama bayan nuna alfahari da kasarsa da yake jagoranta ta Amirka ya kara da cewa:

"Na kuma tsaya a gaban ku a matsayin dan Afirka. Afirka da mutanenta sun taimaka wajen bunkasar Amirka da mayar da ita babbar kasa a duniya, kuma Afirka ta mutanenta sun taimaka wajen inganta lamuran duniya."

Shugaba Barack Obama ya zama shugaban Amirka na farko da ya yi jawabi a helkwatar kungiyar ta Tarayyar Afirka da ke birnin Addis Ababa na kasar Habasha.