Shugaban Amirka George W. Bush, ya isa a ƙasar Vietnam don halartar taron ƙoli na ƙasashen yankin tekun Pacific. | Labarai | DW | 17.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Amirka George W. Bush, ya isa a ƙasar Vietnam don halartar taron ƙoli na ƙasashen yankin tekun Pacific.

Shugaban Amirka, George W. Bush, ya isa a Vietnam don halartar taron ƙolin shekara-shekara kan tattalin arzkin ƙasashen Asiya da na yankin Pacific. Bush dai shi ne shugaban Amirka na biyu da ya taɓa kai ziyara a birnin Hanoi, tun ƙarshen yaƙin Vietnam. An dai sa ran zai yi shawarwari da mahukuntan ƙasar kan inganta harkokin cinikayya tsakanin ƙasashen biyu. Tuni dai shugaba Bush ya yi kira ga ƙasashen APEC ɗin da su farfaɗo da tattaunawar da ake yi kan harkokin ciniki na duniya.

A taron ƙolin kuma, ana kyautata zaton cewa, batun makamshin nukiliyan Korea Ta Arewa, zai kasance ɗaya daga cikin muhimman jigogin da za a tattauna a kansu. Shugaba Bush ya kuma gana da Firamiyan Austreliya John Howard, wanda shi ma ke halartar taron a birnin Hanoi, inda suka tattauana batun halin da ake ciki a Iraqi. Har ila yau dai, Bush zai yi wata ganawa kuma da shugaban ƙasar Sin Hu Jintao, wanda shi ma ya isa a Vietnam don halartar taron.