1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Aljeriya Bouteflika ya yi murabus

Abdullahi Tanko Bala MNA
April 3, 2019

Bayan makonni na zanga-zangar kin jinin gwamnatinsa a karshe Shugaba Abdelaziz Bouteflika na Aljeriya ya yi murabus.

https://p.dw.com/p/3G85z
Algerien Präsident Abdelaziz Bouteflika
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Djarboub

Shugaban kasar Aljeriya Abdelaziz Bouteflika da ke fama da rashin koshin lafiya ya yi murabus daga mukaminsa ba tare da wani jinkiri ba.

Kafar yada labaran kasar ta ruwaito shugaban ya mika wuya ga bukatun masu zanga-zanga bayan shekaru ashirin yana mulkin kasar.

Jama'a sun bazama tituna a Aljiyas babban birnin kasar suna daga tuta da shagulgulan murna.

Gidan talabijin kasar ya ce Bouteflika ya mika bukata a hukumance ga majalisar tsarin mulki ta kawo karshen mulkinsa.

Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian ya ce matakin da Bouteflika ya dauka na sauka daga karagar mulki ya bude wani muhimmin babi a tarihin kasar ta Aljeriya.