Shugaban Afirka ta Kudu zai fuskanci tuhuma | Labarai | DW | 29.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Afirka ta Kudu zai fuskanci tuhuma

Kotun Afirka ta Kudu ta sake bankado tuhumar cin hanci kan Shugaba Jacob Zuma, tuhumar da aka yi watsi da ita a shekara ta 2009.

A wannan Jumma'a kotun kasar Afirka ta Kudu ta yanke matakin cewa ajiye tuhumar da masu gabatar da kara suka yi kan zargin cin hanci da ake wa Shugaba Jacob Zuma a shekara ta 2009 ba ya kan ka'ida. Zuma yana fuskanci tahume-tuhumen cin hanci da rashawa lokacin da aka yi watsi da lamarin cikin shekara ta 2009 bisa zargin akwai hannun gwamnati, yayin da Shugaba Thabo Mbeki yake rike da madafun iko.

Wannan hukunci ya zama koma baya ga Shugaba Jacob Zuma mai shekaru 74 da haihuwa na kasar ta Afirka ta Kudu, wanda sunansa yake kara baci kan shiga abun kunya da ake bankawo na cin hanci da rashawa. Tuni 'yan adawa suka yi maraba da wannan matakin.