Shugaban ƙasar Israila Moshe Katsav na cigaba da fuskantar matsin lamba ya yi mubarus | Labarai | DW | 17.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban ƙasar Israila Moshe Katsav na cigaba da fuskantar matsin lamba ya yi mubarus

Shugaban ƙasar Israila Moshe Katsav na fuskantar ƙarin matsin lamba ta ya yi murabus bayan da yan sanda suka bayar da shawarar tabbatar da tuhumar da ake masa ta aikata fyaɗe da lalata da kuma almundahana. Katsav bai halarci bude zaman majalisar dokoki ba, bayan da yan majalisar suka yi barazanar ƙauracewa zaman muhawarar. Hukumar yan sandan Israila wadda ta shafe tsawon makwanni tana gudanar da bincike a game da zargin, ta baiyana cewa akwai ƙwararan hujjoji da suka tabbatar da cewa shugaban ƙasar ya aikata laifukan da ake tuhumar sa a kan su. Matakin ƙarshe na ga babban Atoni janar na ƙasar. A waje guda kuma P/M Lebanon Fuad Siniora ya yi watsi da gaiyatar da takwaran sa na Israila Ehud Olmert ya yi masa na shawarwarin sulhu. Siniora yace wajibi ne Israila ta fara amincewa da shawarar ƙasashen larabawa ta wanzar da zaman lafiyar wadda tsohon yarima Abdallah na saudiya ya gabatar a shekarar 2003, kafin lebanon ta shiga wata yarjejeniyar sulhu da Israila.