Shugaba Tshisekedi ya gana da Kabila | Labarai | DW | 17.02.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Tshisekedi ya gana da Kabila

A wannan Lahadin ce shugaban Jamhuriyar Demukradiyyar Kwango Félix Tshisekedi ya cimma matsaya da tsohon shugaban kasar Joseph Kabila

A kasar Kwango an kama hanyar kafa gwamnatin gamin gambiza tsakanin jam'iyyun siyasa na bangaren tsohon shugaban kasar Joseph Kabila da kawancen jam'iyyun da suka lashe mulki karkashin jagorancin Felix Tshisekedi. 

Masu aiko da labarai sun ruwaito cewar Kabila ya gana da sabon shugaban Felix Tshisekedi, a wani yunkuri na nada sabon Firaminista karkashin sabon kawancen da za su kafa na siyasa, wanda shi kuma daga bisani zai gabatar da manbobin majalisar ministoci.

Bangaren jam'iyyun siyasar kasar masu goyon bayan Joseph Kabila sun lashe fiye da kashi biyu na adadin kujerun 'yan majalisar dokokin Kwangon 485, a yayin da ita kuma jam'iyyar UDPS ta shugaba Felix Tshisekedi ta samu kujeru 30 a sabuwar majalisar.