1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

An gudanar da bikin tuni da 'yan mazan jiya

Ramatu Garba Baba
November 11, 2020

Wannan shi ne karon farko da Shugaba Donald Trump ke fitowa a bainar jama'a tun bayan shan kayi a babban zaben Amirka. Ya halarci bikin tuni da 'yan mazan jiya da suka fafata a yakin duniya na daya.

https://p.dw.com/p/3lAFl
USA, Shanksville: Donald und Melania Trump während der Trauerminute
Shugaba Donald Trump da mai dakinsa MelaniaHoto: picture-alliance /P. Benic

A karon farko tun bayan shan kayi a babban zabe, Shugaba Donald Trump na Amirka ya halarci bikin tuni da 'yan mazan jiya da suka fafata a yakin duniya na daya. Ya kasance gani na farko da ake ma Trump, da har yanzu ya ki amincewa da sakamakon zaben da abokin hamayyarsa Joe Biden yayi nasara.

Baya ga kin baiyana a bainar jama'a, Mista Trump bai yi wani jawabi ba kamar yadda ya saba yi a baya, face ikirarin da ya ke ci gaba da yi na zargin magudi a shafinsa na twitter tare da shan alwashin kalubalantar sakamakon a kotu.

Tirjiyar ta haifar da tsaiko a shirye-shiryen mika mulki da ka tsara yi a ranar ashirin ga watan Janairun shekara mai zuwa. 'Yan jam'iyyarsa ta Republican na daga cikin wadanda ke rarashinsa kan ya rungumi kaddara, ya kuma mika ragamar mulki cikin kwanciyar hankali. Zababben Shugaba Joe Biden ya lashe zaben na makon jiya inda zai kasance shugaba na 46 na kasar Amirka.