Shugaba Trump ya gana da Sergei Lavrov | Labarai | DW | 10.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Trump ya gana da Sergei Lavrov

Shugaba Donald Trump na Amirka ya gana da ministan harkokin ketaren Rasha Sergei Lavrov a wannan Laraba, wacce ke zama ta farko da wani babban jami'in Rasha ya yi da Mr. Trump din ya yi.

Ziyarar dai na zuwa ne sa'o'i bayan sanar da sallamar shugaban hukumar binciken manyan laifuka ta FBI James Comey, ta tabo batun rikicin kasar Syria, musamman samar da tuddan mun tsira a yankunan kasar da ke fama da yaki. Sai dai shugaban na Amirka ya ce sallamar Mr. Comey ba ta shafi ganawar ta su ba ko kadan.

Bayanai sun yi nunin cewa sallamar jami'in na da nasaba da bincike da ya jagoranta dangane da alakar yakin neman zaben Donald Trump da kuma Rasha. Sai kuma yadda ya yi aiki a kan sakonnin e-mail din 'yar takarar shugabancin kasar karkashin jam'iyyar Democrat da ta sha kayi, wato Hillary Clinton.