Shugaba Trump na ziyara a Koriya ta Kudu | Labarai | DW | 07.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Trump na ziyara a Koriya ta Kudu

A ci gaba da ziyarar aikin da ya soma a wasu kasashen yankin Asiya, Donald Trump na Amirka ya isa a wannan Talata a kasar Koriya ta Kudu inda zai gana da shugaba Moon Jae-In.

Gananawar Trump da Moon Jae-In na da nufin shawo kan sabanin da ke da akwai tsakaninsu musamman kan batun Koriya ta Arewa.

 A watan Satumban da ya gabata ne dai, Shugaba Trump ya zargi takwaransa na Koriya ta Kudu Moon Jae- In wanda ke da ra'ayin sasantawa da Koriya ta Arewa da kasancewa mai gurguwar siyasar neman zaman lafiya maras amfani. 

Sai dai a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter daga kasar Japan inda ya kai ziyarar farko kafin zarcewa zuwa Koriya ta Kudun Trump ya sha alwashin samun fahimtar juna da takwaran nasa wanda a wannan karo  ya bayyana shi da kasancewa mutuman daraja. 

Batun nukiliyar koriya ta Arewa zai kasance a sahun gaban muhimman batutuwan da za su tattauna a kai.