Shugaba Steinmeier na son tazarce | Labarai | DW | 28.05.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Steinmeier na son tazarce

Shugaba Frank-Walter Steinmeier na Jamus ya bayyana aniyarsa ta son samun karin wa'adi na biyu na mulkin kasar don taimakawa Jamusawa.

Dan jam'iyyar SPD da ke cikin kawancen jam'iyyun da ke mulkin Jamus, Steinmeier ya bayyana fatansa na ci gaba da bada tasa gudunmawa wajen sake inganta makomar Jamus da tallafawa mutanen da annobar corona ta yi wa illa sake murmurewa a rayuwa.

Duk da yake jam'iyyarsa ta SPD ta samu koma baya, shugaban da ke kan karagar mulki tun a shekarar 2017 ka iya samun nasarar lashe wani wa'adin mulki idan har ya samu goyon bayan majalisun dokokin kasar biyu na Bundestag da Bundesrat.