1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Afirka ta Kudu ya sha ihu a wurin jana'iza

Ramatu Garba Baba MNA
September 14, 2019

Shugaba Cyril Ramaphosa na kasar Afrika ta Kudu ya sha ihu a yayin da ya shirya yin jawabi a jana'izar tsohon shugaban kasar Zimbabuwe Robert Mugabe a birnin Harare.

https://p.dw.com/p/3Pbt2
Simbabwe Beerdigung von Robert Mugabe
Hoto: AFP/T. Karumba

Ba shiri dai Shugaba Cyril Ramaphosa ya sauya jawabin girmama marigayin ya zuwa na neman afuwar jama'a da suka ki yin shiru har sai da ya nemi gafara kan rikicin kin jinin baki da ya salwantar da rayuka da kuma dukiya a kasarsa wato Afirka ta Kudu. Ramaphosa ya sha suka kan yadda ya gagara shawo kan rikicin na kin jinin duk wanda ba dan kasa ba.

Daga bisani an shawo kan jama'a inda aka ci gaba da gudanar da taron bankwana kamar yadda aka tsara tun daga farko.

Robert  Mugabe ya mutu ne a makon da ya gabata yana da shekaru 95 bayan fama da jinya a wani asibiti da ke a kasar Singapore.