Shugaba Ouattara ya lashe zaben Cote d′Ivoire | Labarai | DW | 28.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Ouattara ya lashe zaben Cote d'Ivoire

Wannan dai shi ne zaben shugaban kasa na farko tun bayan na 2010 wanda sakamakonsa da Tsohon shugaba Gbagbo yaki amincewa da shi ya jefa kasar cikin yanayi na yakin basasa.

Elfenbeinküste Präsidentschaftswahl Alassane Ouattara

Alassane Ouattara na murnar sake nasara a zabe

Shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara ya yi nasarar a zaben da ya gudana ranar Lahadin da ta gabata a kasar, wani abu da ya sake ba shi dama ta ya sake kwashe wasu shekaru biyar na kan karagar mulki a sabon wa'adi.

A cewar Youssouf Bakayoko shugaban hukumar zaben kasar ta Cote d'Ivoire, shugaba Ouattara ya lashe sama da kashi 83 cikin dari na kuri'un da aka kada a zaben da ya gudana ranar 25 ga watan Oktoba.

Shugaba Ouattara dai na bukatar kashi 50 cikin dari ne dan kauce wa zagaye na biyu a tsarin zaben kasar. Sannan babban abokin karawar shugaban wato Pascal Affi N'Guessan ya samu kashi tara ne cikin dari na kuri'un da aka kada. Wannan dai shi ne zaben shugaban kasa na farko tun bayan na 2010 inda shugaba Ouattara ya kada tsohon shugaba Lauren Gbagbo wanda yaki amincewa da sakamakon abin da ya jefa kasar cikin yanayi na yakin basasa da salwantar rayukan dubban jama'a.