Shugaba Obama ya kare shirin Obamacare | Labarai | DW | 04.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Obama ya kare shirin Obamacare

A lokuta da dama Trump ya sha bayyanawa a shafinsa na Twitter cewa shirin inshorar lafiyar na Shugaba Obama annoba ce ga al'ummar Amirka.

Shugaba Barack Obama da mataimakin shugaban kasa mai jiran gado Mike Pence sun yi wani zama da 'yan majalisa a wannan rana ta Laraba, abin da ke zuwa bayan da 'yan majalisa daga bangaren Republican su ka shiga shiri na daukar matakan watsi da shirin inshorar lafiya na shugaba mai barin gado Obamacare.

Shugaba Obama ya zauna da 'yan majalisa dan daukar matakai na kare shirin inshorar saboda irin kalaman na shugaba mai jiran gado Donald Trump wanda ya ce zai watsi da shirin da ma sauya shi da wata dokar.

Shi ma a nasa bangaren Pence ya tattauna da 'yan Republican kan yadda za su yi watsi da shirin na Obama su maye gurbinsa da wani karkashin doka kamar yadda Trump ke muradin gani. A lokuta da dama Trump ya sha bayyanawa a shafinsa na Twitter cewa shirin inshorar na Obama annoba ce.