Shugaba Mursi na Masar na rangadi a Sudan | Labarai | DW | 05.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Mursi na Masar na rangadi a Sudan

A wani abun da ake ganin yana da tarihi, shugaba Mohammed Mursi na Masar ya kai ziyara Sudan domin inganta dangantakar da ke tsakanin kasashen a fuskar tattalin arziki

FILE - In this Friday, July 13, 2012 file photo, Egyptian President Mohammed Morsi speaks to reporters during a joint news conference with Tunisian President Moncef Marzouki, unseen, at the Presidential palace in Cairo, Egypt. Egypt’s Islamist president may hail from the fiercely anti-Israeli Muslim Brotherhood, but in his first major crisis over Israel, he is behaving much like his predecessor, Hosni Mubarak:. He recalled the ambassador and engaged in empty rhetoric supporting Palestinians. Mohammed Morsi is under pressure at home to do more but he is just as wary as Mubarak about straining ties with the United States. (Foto:Maya Alleruzzo, File/AP/dapd)

Shugaba Mohammed Mursi

Shugaban ƙasar Masar Mohammed Mursi ya na ran gadi na wuni biyu a maƙociyar ƙasarsa wato Sudan domin inganta dangantaka ta tattalin arziƙi, a wani abunda ake gani na da tarihi duk da cewa yana zuwa ne kusan shekara guda da zaɓen Morsi a matsayin shugaban ƙasa.

Wannan ce ziyararsa ta farko a Sudan wacce Ƙasar Masar ta mulka tare da haɗin gwuiwar Burtaniya har zuwa shekarar 1956

Ofishin shugaba Mursi, ya ce wannan ziyara na da mahimmanci sosai kasancewar ita ce ta farko irinta, da ma burinta na ƙara danƙon dangantakar da ke tsakanin ƙasahsen biyu musamman a fanin noma, cuɗanya da kasuwanci, da ma mafi mahimmanci yarjejeniyar da suka kira "four freedoms" a turance wacce ta tanadi baiwa, 'yan asalin ƙasashen biyu, 'yancin shiga da fita ƙasashen na su dan gudanar da cinikayya da sauran harkokin da suka danganci bunƙasa tattalin arziƙi.

To sai dai Amurka ta sanyawa Sudan takunkumin kasuwanci tun a shekarar 1997 bisa dalilan da Washington ta ce sun haɗa da take 'yancin bil adama

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Mohammed Awal Balarabe