Shugaba Muhammadu Buhari ya isa kasar Ghana | Labarai | DW | 07.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Muhammadu Buhari ya isa kasar Ghana

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sauka a birnin Accra tare da mai bashi shawara kan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Monguno.

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya isa birnin Accra fadar gwamnatin kasar Ghana a ranar Litinin din nan inda zai gana da shugaba John Dramani Mahama na kasar ta Ghana.

Shugaba Buhari ya sauka a birnin ne na Accra tare da mai bashi shawara kan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Monguno da kuma wasu manyan jami'an gwamnati.

Shugaba Buhari da ya cika kwanaki dari kan karagar mulkin na Najeriya a ranar Asabar a yayin wannan ziyara ta kwana guda cikin batutuwan da za a tattauna sun hadar da batun tsaro da kuma huldar kasuwanci tsakanin kasashen biyu kamar yadda fadar shugaban ta bayyana.

Kafin dai wannan ziyara zuwa Ghana shugaba Buhari ya je kasashen Kamaru da Chadi da Nijer da Jamhuriyar Bene, duka cikin laluben hanyar kawo karshen Boko Haram da tuni ta hallaka mutane sama da 15,000 cikin ayyukanta a Najeriyar da wasu kasashe makwabta.